Polaroid
Uzairu badamasi

BARKA DA ZUWA SHAFI MAI ALBARKA

Alhamdulillah muna muku albishir insha Allah zamu dawo aiki gadan gadan!


Shafin farko

Haidar Ali

Tambayoyi da amsarsu tare da Mallam Ibrahim Zakzaky na daya

Sayyed Zakzaky2

Ina hukuncin wanda ya shafi al'aurarsa alhali yana da alwala?

TAMBAYA: Allah ya gafarta Malam. Menene matsayin bashin nan na Treasury Bills?

SHAIKH ZAKZAKY: To, Treasury Bills, kamar bashi ne wanda mutane ke ba banki, wanda ba shi da wani bambanci da sauran basussuka da aka riga aka sani, wanda su bankunan kan bayar ko a ba su. Wanda in dai da ruwa, to, bai halatta ba, in ba ruwa kuma, to sunansa bashi. In kuma jari ne za a zuba, ya zama ka ci riba. Abin dai da aka sani shi ne, bashi ba ya jawo kudi a shari'a. Kuma jari ne yakan jawo riba ba riba ba.


TAMBAYA: Meye matsayin mutumin da ya hada salloli hudu bai yi su ba sai da asuba ya hada su gaba daya? Shin yana da sallar ko ba shi da ita, kasantuwar lokacinta ya wuce? Daga Sani Musa Ali Jos

SHAIKH ZAKZAKY: To, ya aikata haram. Domin bai halatta ga musulmi mai hankali baligi ya bari lokacin salla ya wuce bai yi sallar ba. Sai dai in ya yi, ba za a ce ba shi da salla ba don lokacin ya wuce, domin tana nan a kansa. Ana ce wa wannan ramuwa. Lalurar da kawai ke iya halatta mutum ya jinkirta salla har lokacinta ya wuce shi ne, rashin abubuwan tsarkin nan guda biyu, wato ruwa da kasa, wanda idan babu su, ba abin da zai yi illa ya kyale in lokaci ya wuce sai ya biya. Wannan kuma ba laifi bane. Sai kuma lalurar rashin hankali, wanda idan da barci ne, alal misali, shi ma in ya farka sai ya biya. In kuma hauka ne ko suma in har ya cika lokacin salla din, to, shi ma sallar ta fadi a kan sa. Saboda haka, haka kawai bai halatta ma mutum ya fasa salla ba har lokacinta ya wuce. Amma in ya yi haka nan ya yi haram, kuma in ya yi salla din bayan lokacinta, ta yi. Kuma ma ta hau kansa ya biya komi dadewa.

TAMBAYA: Akramakallahu, shin idan mutum ya sami dama yana iya zuwa ya kai wa musulmi taimako akasashen da kafirai ke yaki da muslmi, misali Falasdinu ko Iraki? Daga Salisu Ali Yarima Mile 12 Lagos

email.salisuyarima2000@yahoo.com TEL 08033304133.

SHAIKH ZAKZAKY: To, lalle ban san shi abin da yake nufi ba. Wala'alla yana nufin kai gudummawa na kudi ne. Wanda ba ya bukatar sai ya tashi takanas ya tafi da kansa ya kai wannan gudumawa din. Akwai hanyoyi da daman gaske budaddadu na aikawa da gudummawa, musamman dai Palasdinu, kuma zai wahalar gaske ya zama shi (mai tambaya din in shi ne yake so ya kai), ya zama zai iya zuwa wadannan wurare da ya ambata don ya kai wata gudummawa, ko ma wace iri ce. Amma dai yana iya bayar da gudummawarsa daidai gwargwadon hali yana zane a nan ba tare da ya tafi can ba. In wannan yake nufi, to, sai mu ce masa eh, yana da kyau haka nan. Sai ya yi musharaka da dukiyarsa a yayin da ba zai yiwu ya yi musharaka da jikinsa ba.

TAMBAYA: Assalamu alaikum. Menene hukuncin tuka mota ga matar aure?

Daga Hadiza Shu'aibu Kalanbaina Sakkwato

SHAIKH ZAKZAKY: To, ba wani abin da aka samu dangane da wannan. Sawa'un matar aure ce ko wadda ba ta yi aure ba, wadda ba ta da miji. Saboda haka, a shari'a kuwa, asalin komai shi ne halasci sai in haramci ya zo. Kuma abin da ba a haramta maka ba, ya halatta. Saboda haka in dai hukunci ne, to, sai mu ce halas ne, matar aure ko ba matar aure ba, babu bambanci a nan. Mace in tana da aure ko ba ta da aure dangane da tukin mota.

TAMBAYA: Allah ya gafarta Malam. Ina hukuncin wanda ya shafi zakarinsa alhali yana da alwala?

SHAIKH ZAKZAKY: To, ba wani abin da ya hau kansa. A Malikiyya an ce alwalarsa ta baci, dogaro bisa wata riwaya wacce aka ce, wani cikin magabata yana ma wani shiftar Alkur'ani, sai ya ga ya yi susa, sai ya ce, "ko ka taba al'aurarka?" Ya ce eh! Sai Malamin ya ce masa, "tashi ka yi alwala." A kan wannan ne. Kuma wanda su Malikiyyar ne kawai koma bayan sauran Mazhabobi suke da wannan ra'ayin, duk sauran mazhabobi ba su da wannan ra'ayin. To, shi ma a Malikiyan in muka koma, za a ga cewa shi kansa wannan riwaya din, muna iya cewa, wannan wurin, babu inda aka ji shi. Duk sauran mazhabobi ba su san da hadisin ba, ba su kuma san daga ina aka samo shi ba. Saboda haka abin da za mu iya cewa shi ne, a Malikiyya suna cewa haka nan, kodayake shi ma ba dogaro bisa wani hujja kakkarfa ba. Amma sauran mazhabobin Musulunci ba su san da haka nan ba.

TAMBAYA: Assalamu alaikum.Dan uwa ne yake aiki a Hukumar wutar lantarki ta kasa NEPA, sai aka ajiye shi a fannin yanke wuta. Shin idan ya yanke wutar wadanda ba su biya ba, ya yi zunubi? Kuma wani lokaci idan mun yanke wutar, akan bi mu a ba mu wasu 'yan kudi don mu mayar masu da wutar tasu. Shin muna iya mu mayar. Kuma idan da ma mun taba cin irin wannan kudin, to, menene matsayinsu?

Daga Kabir Ibrahim Kukkumake, Kaduna.

SHAIKH ZAKZAKY: To, shi dai aiki kamar yadda aka sani yana da ka'ida. Saboda haka su ma'aikatar da suka dauke ka aiki, da ma suna da ka'idojinsu, kuma a kan wadannan ka'idojin ne suka dauke ka aiki. In ka ga abin da ya saba wa shari'a a ka'idojin nasu, to, da ma tun farko ba za ka yi aikin ba. Kuma idan yana ganin shi a fahimtarsa bai kamata a je a yanke wa mutane wutar lantarki ba, saboda zalunci, to tun farko ba zai yi aikin bane, saboda su abin da suke yi kenan. Na'am, muna iya cewa, na farko dai, ba shi mai yanke wutar ba, ita NEPA din, ya kamata a ce ta yanke wutar lantarkin mutane? Sai mu ce lalle bai kamata ba. Ta wata fuskar ma ana iya cewa bai halatta ba, ganin cewa da wuta da ruwa, duk hakkoki ne na al'umma. Kuma a wannan lokaci namu, duk al'ummomin duniya suna samar wa al'ummunsu da wadannan a cikin kudade saukaka. Wanda sauran al'ummu ba za taba sawwala cewa za a iya zuwa a yanke masu ba. Sai dai ta yiwu ita Hukuma din ta san su mutane mabukata ne ga wadannan abubuwa, ruwa da wuta sai ta sami hanyar da ta bi wajen karbar kudinta daga wajensu, amma ba ta hanyar yanke masu ba. Saboda haka idan ya zama ka'idar aikin da ma ya ga ya saba, kuma ba zai yi ba, zai bar aikin ne. Sannan kuma kudaden da suke karba (su ma'aikatan), shi ma zai kasance yana da matsayi a ka'idar aikin nasu ai. Idan sun karbi kudin da ma wa suke ba? Suna mayarwa ne cikin aljihun NEPA, ko kuwa aljihunansu? Idan aljihun NEPA ne, to, shike nan in zalunci ne, ya taimaka masu wajen zaluntar al'uuma, idan kuma aljihunsu suke zubawa, to, sai a tambaye su har wal yau, a bisa ka'ida da ma wadannan kudaden a aljihunansu ya kamata ya shiga? Idan eh ne, to shike nan halak malak, sai ya ci abinsa.

TAMBAYA: Assalamu alaikum. Na gani a ayyukan daren Juma'a, Imam Sadik (AS) ya ce, duk wanda ya yi waka ko da a kan gaskiya ne, to ba shi da ladan ayyukan wannan ranar. Sai kuma na ga ana shirya majalisin mawaka a ranar ko daren. Yaya abin yake?

Daga Nasiru Ibrahim Shanono, Kano

SHAIKH ZAKZAKY: To, hukuncin yin wake a daren Juma'a da ranarta, shi ne karhanci. Wannan kuma ko ba komai yana nufin lalle waken da ya halatta ne a yi a sauran ranaku da darare. Amma saboda muhimmancin daren Juma'a da kuma ranar Juma'a, don mutum ya shagalta da ayyukan ibada ma'asurai, shi ya sa sai aka karhanta masa yin wadannan. Kuma ba kamar yadda shi (mai tambayar ) ya fada ba, abin da hadisin ya ce shi ne; "lam yakun lahu nasibun siwahu fi tilkall lailati," ko abin da ya yi kama da haka nan. Abin da yake cewa shi ne, ba shi da wani lada sai wannan, a wannan dare ko wannan yini, wato wannan waken. Wato maimakon ka yi salloli da addu'o'i, sai ka yi wake, to, waken ne ladanka. Ka ga ka yi hasarar ladan wadancan ma'asurai. Wannan yana daga cikin abin da ake ce wa, a hanaka abu karami don ka yi babba. Shi waken, ba haramun bane, duk ya halatta. Amma addu'ar ta fi, salloli da addu'o'i sun fi wake. saboda haka wanda ya yi wake, ladan waken ya samu. Ka ga ya yi asarar salloli da addu'o'in da bai yi ba. Amma ba yana nufin wai haramun ne ba.

TAMBAYA: Assalamu alaikum. Ina da kudi kuma sai nan da wata hudu zan yi amfani da su. Shin ya halatta in sayi amfanin gona in ajiye, ko bai halatta ba?

Daga Nasiru Ibrahim Shanono, Kano

SHAIKH ZAKZAKY: To, abin da ya haramta dangane da sayen abinci a ajiye shi ne, in ya kai haddin da ake ce masa 'Ihtikari,' shi ne boye abinci alhali al'umma tana bukata. In kayan abincin da zai saya ya ajiye din, al'ummar musulmi ba za su bukatu ya zuwa gare su ba, ta yadda shi sayen da ya yi ya boye zai cutar da su ba, to babu komai. Wato in bai kai haddin 'Ihtikari' ba, babu komai.

TAMBAYA: Assalamu alaikum. Mace tana yi mani sallama kuma ba muharrama ta ba ce. Ya halatta na amsa?

Daga Sadisu A Sani Babban Rami jihar Katsina

SHAIKH ZAKZAKY: Eh, ya halatta in dai sallama din ne. Hatta ma in kana saye da sayarwa, ya halatta ku yi ciniki, ta taya ka ce albarka, har ku daidaita a cinikin. Wato a kan maganar da ya halatta, ka yi da ita, ya halatta ka yi da ita, wanda ya haramta ne ya haramta.

TAMBAYA: Menene hukuncin yin sujada a kan siminti ko a kan kwali?

Daga Sadisu A Sani Babban Rami jihar Katsina.

SHAIKH ZAKZAKY: To, halacci ne, wato mutum yana iya yin sujada a kan siminti, ko a kan kwali. Sai dai ba zai iya yin taimama a kan kowanne daga cikinsu ba.

TAMABAYA: Ko akwai fifiko tsakanin 'yan uwa masu gwagwarmaya na kauye da na birni?

SHAIKH ZAKZAKY: To, ayyukan ibada, Allah (T) yana ba da sakamakonsu ba ya la'akari da cewa ko kai bakauye ne ko kai babirne ne. Aikin da ka yi ne za ka sami lada. Wala'alla kila wani aikin ya zama ya fi lada in an yi shi a kauye fiye da birni, wani kuma tana iya yiwuwa ya zama in an yi shi a birni ya fi lada fiye da a kauye. Ya danganta da aikin ne. Amma ladan ba shi da dangantaka da kauye ko da birni. Aikin ake la'akari da shi, ba wai mutum ina ya yi aikin ba.

TAMBAYA: Shin ya halasta dan uwa ya rikayin wasan nan na SNOOKER?

Daga Abubakar Saleh Badikko Kaduna.

SHAIKH ZAKZAKY: To, shi dai wasan Snooker, ba wani abin da aka sani dangane da haramci a kansa. Kuma kamar yadda na sha nanatawa, abin da ba a hana ka ba, to, shi kenan ka na iya yi, sai dai idan ya shiga eriyar da za a ce masa wargi, 'Lagawu,' banzantar da lokaci, to, shi kuma ya san wannan. Kowanne irin wasa yana iya fita haddin da ya halatta, ko da ma halas din ne. Wato in ya zama ya kai ma yana cinye lokaci da kuma shagalta da shi koma bayan ayyukan kirki.

TAMBAYA:Shin mutum zai iya cin yankan arnan kasar nan, kuma zai iya cin abincinsu, tun da ana ce da su Ahlul kitabi?

Daga Abubakar Saleh, Badikko Kaduna.

SHAIKH ZAKZAKY: To, ban san abin da yake nufi da arnan kasar nan ba, domin kalmar arna ba kalma ce ta addini ba. In yana nufin kiristoci ne, to sai mu ce, mu a tamu fahimtar, ko da aka halatta mana cin abincin Ahlul kitabi, ba a halatta mana cin yankan su ba. Kodayake akwai sabanin ra'ayi a wadansu mazhabobi. Wasu na ganin cewa abin da suka yanka na abin da ya halasta masu su su ci, to, mu ma muna iya ci. Amma sun yanka domin su su ci ne, ba domin mu mu ci ba. Amm mu a fahimtarmu lallai wannan din ma bai halatta ba. Sai dai abincinsu da ya halatta a wajenmu, sune abin da bai shafi yanka ba, kamar kwaya (tsaba), ko 'ya'yan itatuwa, ko wani abin da ya yi kama da haka nan. Amma ba abin da suka yanka ba, ko da ya halatta mana ya halatta masu. Ballantana ma akasin haka

.
Copyright © 2018~2022.
( Uzairu Badamasi Sufi )
Harkarmusulunci@yahoo.com
All rights reserved

Bamu Da Alhakin Tallar Da Ake Sawa Akan Wannan Website Din